Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jarin kai tsaye na ketare da aka zuba a kasar Sin daga Janairu zuwa Yuli ya karu da kaso 7.3
2019-08-13 11:10:02        cri

Ma'aikatar cinikayyar kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, jarin kai tsaye na ketare da aka zuba a babban yankin Sin, daga watan Janairu zuwa Yulin wannan shekara, ya kai Yuan biliyan 533.14, karuwar kaso 7.3 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.

Ma'aikatar ta ce, a bangaren dalar Amurka kuwa, jarin ketaren da aka zuba ya karu zuwa kaso 3.6 cikin 100, wato Yuan biliyan 78.8 bisa makamancin lokaci na bara.

Kana a watan Yuli kadai, jarin kai tsaye na ketare da aka zuba a babban yankin kasar Sin, ya kai na Yuan biliyan 54.82, karuwar kaso 8.7 cikin bisa na makamancin lokaci na bara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China