Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin Hong Kong ba ta ji dadin kalaman wasu 'yan Hong Kong a hukumar Amurka mai zaman kanta dake sa ido kan yadda ake kare hakkin bil Adam da raya dokoki a kasar Sin ba
2019-09-19 14:02:10        cri
A ranar 17 ga wata, wasu 'yan yankin Hong Kong na kasar Sin sun yi jawabi a hukumar Amurka mai zaman kanta dake sa ido kan yadda ake kare hakkin bil adam da raya dokoki a kasar Sin, inda suka yi zargin karya kan zanga-zangar nuna karfin tuwo da aka gudanar a cikin 'yan kwanakin da suka wuce a Hong Kong, kana sun kalubalanci majalisar dokokin Amurka da ta zartas da daftarin dokar kare hakin bil Adam da tsarin demokuradiyyar Hong Kong.

Game da haka, kakakin gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ya nuna bakin ciki sosai a kai, ya kuma jaddada cewa, bai kamata ba majalisun dokokin kasashen waje su tsoma baki a cikin harkokin yankin Hong Kong.

Baya ga haka, kakakin ya bayyana cewa, tun bayan da yankin musamman na Hong Kong ya dawo hannun kasar Sin, yankin yake baiwa jama'arsa damar gudanar da harkokinsu bisa 'yancin doka da tafiyar da harkokinsa kamar yadda doka ta tanada, ana iya cewa, an cimma nasarar tabbatar da tsarin nan na kasa daya, tsarin mulkin biyu. Kana ana tabbatar da kare 'yanci da hakkin bil Adama a yankin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China