Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayar da tallafin kayayyakin zamanantar da aikin gona ga Habasha
2019-08-17 15:14:17        cri
A jiya Juma'a gwamnatin kasar Sin ta bayar da taimakon kayayyakin aikin gona iri daban daban kimanin 136 ga kasar Habasha, a matsayin wani bangare na tallafin kasar Sin ga kasar Habasha domin bunkasa tattalin arzikin kasar ta fannin aikin gona.

A lokacin bikin mika tallafin, Tan Jian, jakadan Sin a kasar Habasha, ya bayyana cewa, tallafin kayayyakin da kasar Sin ta baiwa Habasha wani bangare ne na yunkurin tallafawa kasar Habashan domin zamanantar da fannin aikin gona.

Jakada Tan ya ce, taimakon da Sin ta baiwa Habasha wajen zamanantar da aikin gonar wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwar bunkasa ci gaba tsakanin kasashen biyu.

Ministan aikin gonan kasar Habasha Oumer Hussien ya ce, tallafin sabbin kayayyakin aikin gonan da kasar Sin ta bayar wani bangare ne na yunkurin cimma burin gwamnatin Sin wajen tallafawa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Habasha.

Hussien ya ce, shirin tallafin da kasar Sin ta baiwa fannin aikin gona ga kasar Habasha yana da matukar muhimmanci musamman ga bangarorin samar da horo, fasahar zamani, da kuma musayar kwarewa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China