Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Habasha sun saki mutane 57 da aka tsare bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulki
2019-07-28 16:32:12        cri

Gwamnatin kasar Habasha ta sanar a ranar Asabar cewa ta saki wasu mutane 57 wadanda ake tsare da su bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan jiya, kafar watsa labaran kasar (FBC) ne ta bada rahoton.

Mutanen 57 an tsare su ne bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin ranar 22 ga watan Yuni, wanda ya yi sanadiyyar kashe rayukan wasu sojojin kasar Habashan da fararen hula.

FBC ta rawaito cewa, an saki mutanen 57 ne bayan rashin samun kwararan hujjoji dake tabbatar da cewa suna da hannu a yunkurin juyin mulkin.

A farkon wannan watan, kasar Habasha ta saki wasu jami'an tsaro 113, wadanda da farko aka zarge su da hannu a yunkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba.

Jami'an tsaron 113 wadanda dukkansu jami'an 'yan sandan musamman ne da suka fito daga shiyyar arewacin jahar Amhara, an sake su bayan kammala bincike inda gwamnatin kasar Habashan ta wanke su daga duk wani zargin aikata ba daidai ba.

Yunkurin juyin mulkin na ranar 22 ga watan Yuni wanda bai samu nasara ba, an zargi dakarun tsaron kasar dake biyayya ga Asaminew Tsige, tsahon babban jami'in tsaron jahar Amhara, ya yi sanadiyyar kashe rayukan mutane masu yawa ciki har da shugaban jahar Amhara Ambachew Mekonnen, da babban hafsan tsaron rundunar sojojin kasar Habashan, Seare Mekonnen. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China