Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha ta samu dala miliyan 142 daga yankin masana'antu da Sin ta gina a kasar, in ji wata jami'ar kasar
2019-08-09 10:58:35        cri
Kasar Habasha ta samu kudaden shiga da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 142, daga hada hadar fitar da kayayyaki, albarkacin yankin masana'antu da kasar Sin ta gina a kasar. Mataimakiyar kwamishina mai lura da harkokin zuba jari a kasar Hana Arayaselassie ce ta bayyana hakan, tana mai cewa, wannan kudade kasar ta same su ne tsakanin shekarar 2018 zuwa watan Yulin shekarar nan ta 2019.

Kaza lika kafar watsa labarai ta kasar ENA, ta rawaito Arayaselassie na cewa, layin dogo mai aiki da lantarki da kasar Sin ta gudanar, aka kuma kaddamar a watan Janairun shekarar 2018, wanda ya hada kasar Habasha da Djibouti, ya taimaka matuka wajen bunkasa damar Habasha ta fitar da hajojin ta zuwa kasuwannin ketare. Hakan ya samu ne sakamakon damar fitar da sundukan dakon kaya cikin sauri daga yankin masana'antun kasar dake babban yankin Habasha, zuwa tashar jiragen ruwa dake Djibouti.

Jami'ar ta kara da cewa, dunbin kudaden da kasar Habashan ta samu a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2019, sun haura na shekarar 2017 zuwa 2018 da kusan kaso 50 bisa dari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China