Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an MDD da wakilan wasu kasashe sun taya wa kasar Sin murnar cika shekaru 70 bayan kafuwarta
2019-09-22 16:21:20        cri
A daren ranar 20 ga wata, zaunanniyar tawagar kasar Sin dake MDD ta kira liyafa don taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, inda wasu manyan kusoshi na MDD da wakilan kasashe daban daban suka yaba ma kasar Sin kan nasarorin da ta samu a fannin raya kasa, da gudunmowar da kasar ta samar ta fuskar kiyaye zaman lafiya a duniya, gami da kokarin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba.

Yayin da yake jawabi a wajen liyafar, mataimakin babban magatakardan MDD mai kula da aikin wanzar da zaman lafiya, Jean-Pierre Lacroix, ya ce, yana farin cikin ganin Majalisarsa na samun goyon baya daga kasar Sin, yayin da take kokarin tinkarar kalubale daban daban. A cewar Lacroix, 'yan sandan kasar Sin dake gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a wurare daban daban na duniya, suna kokarin kare fararen hula, da tabbatar da tsaro, da gina kayayyakin more rayuwa, gami da neman kyautata zaman rayuwar jama'ar wuraren, inda suke samar da babbar gudunmowa ga aikin wanzar da zaman lafiya a duniya.

A nata bangare, darektar zartaswa ta Asusun kula da Yara na MDD UNICEF, Henrietta H. Fore, ta ce kasar Sin na kokarin cimma burikan da ta sanya cikin shekaru 10 masu zuwa, wadanda suka hada da sanya kashi 85% na kananan yara 'yan kasa da shekaru 6 cikin makarantu zuwa shekarar 2020, da dai sauransu. Matakan, a cewar jami'ar, za su amfanawa yaran kasar sosai.

Ban da haka, a nashi bangare, zaunannen wakilin kasar Rasha a MDD Vasily Nebenzya ya ce, kasar Sin ta samu babban ci gaba cikin shekaru fiye da goma da suka wuce, ta yadda ta zama daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arzikin duniya. A cewarsa, an kulla hulda tsakanin kasashen Sin da Rasha ne bisa tushen girmama juna, da aminci, wadda ke taimakawa tabbatar da kwanciyar hankali a duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China