Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun Afrika sun bukaci a hada gwiwa wajen magance manyan kalubalolin masana'antu
2019-07-02 11:20:58        cri

An bukaci kasashen Afrika da cibiyoyin Afrika da su hada gwiwa wajen tunkarar manyan kalubalolin dake shafar fannin masana'antu.

Wasu kwararrun Afrika da masu tsara dabarun cigaba a yayin da suka gudanar wata tattaunawa sun bukaci a gaggauta daukar matakan aiwatar da yarjejeniyar ciniki marar shinge tsakanin kasashen nahiyar Afrika wato (AfCFTA), wacce aka amince da ita a Addis Ababa na kasar Habasha a ranar Litinin, inda suka bayyana yarjejeniyar cinikin tsakanin kasashen nahiyar da cewa muhimmin cigaba ne wanda zai kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen nahiyar domin tunkarar manyan kalubalolin dake damunsu.

Parfait Onanga, wakilin MDD dake Afrika, wanda ya bayyana cewa, har yanzu nahiyar Afrika tana da shinge, inda ya bukaci kasashen na Afrika su yi aiki tare muddin suna fata da burin samun nasarar magance manyan kalubaloli dake damun nahiyar, musamman ta fuskar cigaban masana'antu.

"Muna bukatar kara kaimi wajen tunkarar manyan matsalolin dake damun nahiyar," inji wakilin MDD, ya kara da cewa, "Ya kamata mu gane cewa babu wata kasa da za ta iya magance kalubalolin da ake fuskanta a karni na 21 ita kadai. Muna bukatar yin aiki tare da juna ta hanyar amfani da muhimman matakai kamar yarjejeniyar AfCFTA domin samun kyakkyawan sakamako tare."(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China