Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawarar "ziri daya da hanya daya" ta samar da sabuwar damar samun ci gaba ga duk duniya
2019-10-05 16:15:17        cri
A yayin cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi sau da dama, inda ya jaddada cewa, jama'ar Sin za su yi kokari tare da jama'ar duniya wajen sa kaimi ga raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama tare. Wannan ne shirin Sin game da sa kaimi ga samun ci gaba cikin lumana da sarrafa harkokin duniya. A lokacin kaka na shekarar 2013, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, wadda ta nemi sabuwar hanyar bunkasa tattalin arzikin duniya, da samar da gudummawa wajen warware matsalar rashin daidaito kan bunkasuwar duniya, don hakan shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasance muhimmiyar hanyar kyautata harkokin duniya.

An jaddada cewa, a cikin shekaru 6 da suka gabata, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta zama kamar tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, wadanda dukkansu sun kara yin imani da juna da hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannonin tattalin arziki da al'adu. Ya zuwa karshen watan Yuli na bana, kasashe 136 da kungiyoyin kasa da kasa 30 sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa don raya shawarar "ziri daya da hanya daya". An rubuta tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama a cikin kudurorin MDD sau da dama, wannan ya shaida cewa, tunanin ya dace da tunanin MDD na shimfida zaman lafiya tare, wanda ya nuna makomar duniya mai kyau tare da dacewa da moriyar kasa da kasa. Manazarcin kwalejin kula da harkokin siyasa da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa na jami'ar Cambridge ta kasar Birtaniya Martin Jacques ya yi nuni da cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta hada kyakkyawar makoma da matakan da aka dauka don cimma wannan makoma, tana da babbar ma'ana, babu shakka za ta cimma nasara. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China