Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Aikin nazari kan ilmin kimiyya yana tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin Sin cikin sauri
2019-09-30 12:21:17        cri
A halin yanzu, kasar Sin kasa ce ta biyu a karfin tattalin arziki dake mai da hankali kan zuba jari, a fannin nazari kan ilmin kimiyya, bayan kasar Amurka wadda take ta farko a wannan aiki.

Cikin shekaru 6 da suka gabata, kasar Sin tana da ma'aikata masu nazarin ilmin kimiyya mafi yawa a duk fadin duniya, kana, tana kan gaba cikin shekaru 8 da suka gabata a fannin samar da lambobin kira, lamarin da ya sa, Sin ta kasance babbar kasa mai ikon mallakar ilmi.

An fidda manufar raya kasa ta hanyar yin nazari kan ilmin kimiyya tun daga shekarun 1990 na karnin da ya gabata. A halin yanzu kuma, Sin ta tsara burin kafa wata kasa mai karfi a fannin kimiyya da fasaha. Cikin wadannan shekaru da suka gabata, Sin ta dukufa wajen yin nazari kan ilmin kimiyya, yayin da take kiyaye ikon mallakar ilmi yadda ya kamata. Saboda haka ne Sin ta sami bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, a wadannan shekaru bisa muhimmiyar rawar da ta taka a fannin yin nazari kan ilmin kimiyya, da kuma sabbin fasahohi da kayayyakin da ta samar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China