Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara kokari shi ne hanyar da ta dace wajen girmama jarumai
2019-09-29 16:53:15        cri
A yau 29 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da lambobin yabo na jamhuriyar kasar, da na sada zumunci da na karramawa na kasa ga mutanen Sin da baki 42. Xi Jinping ya yabawa mutanen da suka samu lambobin. Yana mai cewa, sun kasance masu gaskiya da juriya, wadanda suka dace da ra'ayin Sinawa kan halin jarumtaka, da tunanin al'umma.

Ya ce "jama'a na cike da imani, kuma kasa na cike da fata, kana al'umma na cike da karfi" ga Sinawa kusan biliyan 1.4, a yayin da suke koyi da wadannan mutane da suka samu lambobin yabo. Ya ce kamata ya yi a yi amfani da hallayarsu ta tsare gaskiya da juriya kan zaman rayuwa, don samun karfin ciyar da kasar gaba, da sa kaimi ga wayewar kai, da kuma raya wata duniya mafi kyau, da nufin cimma burin farfado da al'ummar kasar Sin, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga 'yan Adam. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China