Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Sin mai bin hanyar ci gaba cikin lumana ta zama mai karfafa kwanciyar hankalin duniya
2019-09-30 20:37:09        cri

A ranar 30 ga wata, an wallafa sharhi mai taken "Sin mai bin hanyar samun ci gaba cikin lumana ta zama mai karfafa kwanciyar hankalin duniya".

Sharhin ya nuna cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, yayin da jama'ar Sin ke raya kansu bisa manufar dogaro da kai da yin gwagwamaya cikin himma da kwazo, suna kuma ba da taimako ga zaman lafiya da ci gaban duniya. Yadda Jamhuriyar Jama'ar Sin ta samu bunkasuwa cikin shekaru 70 da suka wuce ya shaida cewa, kasar Sin mai bin hanyar samun ci gaba cikin lumana ta ba da gudummawa ga samun zaman lafiyar duniya a fannoni daban daban, haka kuma sakamakon kasancewar kasar Sin, duniya ta kara samun kwanciyar hankali.

Ban da wannan kuma sharhin ya jaddada cewa, yadda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da watsi da tsarin mulkin danniya da kasashe masu matukar karfi kan yi, da ma neman hadin kan kasa da kasa don moriyar juna da samun nasara tare, ba ma kawai wannan ya sauya salon da manyan kasashe kan bi wajen samun farfadowa cikin daruruwan shekaru da suka gabata ba, har ma ya yi muhimmin tasiri ga makomar ci gaban duniya. A matsayinta na kasa da ke nacewa ga samun bunkasuwa cikin lumana don samun farfadowar al'umma, kome karfin da kasar Sin ta samu, ba za ta kawo barazana ko kadan ga ko wace kasa ba, sai dai samar musu babbar dama mai kyau. Burin kasar Sin a koda yaushe, shi ne karfafa kwanciyar hankalin duniya.(Kande Gao, ma'aikaciyar sashen Hausa na CRI)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China