Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Kokarin kare 'yancin mallakar fasaha na taimakawa raya tattalin arzikin Sin
2019-10-01 21:26:22        cri
A shekarar 1980, kasar Sin ta shiga hukumar kare 'yancin mallakar fasaha ta duniya, daga bisani ta sa hannu kan yarjeniyoyi daban daban masu akala da aikin kare 'yancin mallakar fasaha. A kokarin kare wannan 'yanci, kasar Sin ta samu damar sanya kaimi ga aikin kirkiro sabbin fasahohi, da kare hakkin kamfanonin kasashen ketare dake zuba jari a kasar Sin, gami da karfafawa al'ummun kasar gwiwar shiga aikin raya kimiyya da fasaha. Yanzu kasar Sin na sauya matsayinta daga kasar dake martaba ka'idojin kare 'yancin mallakar fasaha kawai, zuwa kasar dake jagorantar wannan fanni a duniya. Wannan kokari zai taka muhimmiyar rawa a yunkurin da kasar ke yi na kara inganta masana'antunta. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China