Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye muhallin duniya
2019-09-30 15:00:28        cri

A jiya ne, aka gudanar da taron manema labaru na 4, a cibiyar watsa labaru ta bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, inda ministan ma'aikatar kiyaye muhallin kasar Sin Li Ganjie ya bayyana cewa, a cikin shekaru 70 da suka gabata, Sin ta samu manyan nasarori kan sha'anin kiyaye muhallin kasar. Musamman bayan taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 18. Sin ta shiga aikin kiyaye muhallin duniya, da gabatar da shirin kasar Sin na aiwatar da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030, wanda ya jagoranci, da yin yunkurin yin shawarwari kan sauyin yanayin duniya. Kana Sin ta kasance mai shiga a dama da ita, da mai samar da gudummawa, da bada jagoranci na aikin kiyaye muhallin duniya.

Batun magance gurbatar iska yana da nasaba da zaman rayuwar jama'a, wanda ya jawo hankalin jama'a sosai. A shekarun baya baya nan, an kyautata yanayin iska na kasar Sin sosai. Dangane da batun, ministan harkar kiyaye muhallin kasar Sin Li Ganjie ya bayyana cewa,  

"Alal misali, matakin wasu abubuwa masu gurbatar iska mai lakabin PM 2.5. Shekarar 2013 ita ce shekara ta farko da muka tsara ka'idoji 10, don yaki da gurbatar iska. A cikin shekaru 6 da suka gabata, an rage yawan PM 2.5 a birane 74 da aka yi binciken iska a can, wanda ya kasance karo na farko a kasar Sin, da kashi 41.7 cikin dari. Musamman a birnin Beijing, yawan PM 2.5 na birnin ya ragu da kashi 43 cikin dari. Wannan ya shaida cewa, mun samu babbar nasara a wannan fanni."

Li Ganjie ya kara da cewa, yawan kwanakin da aka fi samun gurbatar yanayin iska ya ragu sosai. Idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, kasar Sin ta fi dora muhimmanci, da yin kokarin kyautata muhallin kasar a wadannan shekaru.

A cikin shekaru 70 da suka gabata, Sin ta bi tunanin kiyaye muhalli don amfanin jama'a, da kawo moriya ga jama'a. An kara kiyaye muhalli da kyautata muhalli, da tsara tsarin kiyaye muhalli bisa dokoki yadda ya kamata. Ta hakan aka samu babban ci gaba kan kiyaye muhallin kasar Sin. Mataimakin minista mai kula da aikin kiyaye muhallin kasar Huang Runqiu ya bayyana cewa,

"A cikin shekaru 70 da suka gabata, an kafa yankunan kiyaye muhallin halittun kasar Sin guda 2750, fadin yankunan ya kai muraba'in kilomita miliyan 1 da dubu 470, wanda ya kai kashi 15 cikin dari bisa adadin fadin kasar Sin. Ban da wannan, yawan yankunan kiyaye muhalli iri daban daban na kasar Sin ya kai 11029. Kana fadin adadinsu duka ya kai kashi 18 cikin dari bisa na dukkan yankunan kasar. Hakan ya bayyana cewa, an cimma burin habaka fadin yankunan kiyaye muhalli don ya kai kashi 17 cikin dari nan da shekarar 2020, bisa yarjejeniyar kiyaye halittu iri daban daban ta MDD."

Huang Runqiu ya kara da cewa, a shekarar 2020, kasar Sin za ta dauki bakuncin taro na 15, na masu daddale yarjejeniyar kiyaye halittu iri daban daban ta MDD. Taken taron shi ne "Kiyaye muhalli don raya rayuwa ta dukkan duniya baki daya", wanda ya shaida cewa, kasa da kasa sun nuna amincewa ga nasarorin da Sin ta samu a fannin kiyaye muhalli, da raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba.

Samun ci gaba ba tare da gurbata yanayi ba, yana daya daga cikin manyan tunanin raya kasar Sin. Bayan da aka gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin raya kasa ba tare da gurtaba yanayi ba, don sa kaimi ga aiwatar da shawarar.

Minista Li Ganjie ya bayyana cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" hanya ce ta samun bunkasuwar tattalin arziki da wadata, kana ta samun bunkasuwa ba tare da gurbata yanayi ba. Ya ce, an shigar da aikin kiyaye muhalli a cikin ayyukan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", sai dai za a tafiyar da shawarar a dogon lokaci yadda ya kamata. Li ya bayyana cewa,

"Mun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa fiye da 50 tare da hukumomin kiyaye muhalli na kasashen dake bin shawarar 'ziri daya da hanya daya', da na kungiyoyin kasa da kasa. Kana mun kafa kawancen samun bunkasuwa ba tare da gurbata yanayi ba na kasashe masu bin shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Ya zuwa yanzu, hukumomin gwamnatocin kasa da kasa, da kamfanoni, da kungiyoyin masana, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 130 sun shiga kawancen, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' ba tare da gurbata muhalli ba."

Li ya kara da cewa, a mataki mai zuwa, za a kara yin shawarwari tare da kasashe masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" a fannin tsara manufofi da ma'auni, tare da horar da kwararru don sa kaimi ga raya shawarar, musamman bada gudummawa ga raya shawarar ba tare da gurbata yanayi ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China