Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gabatar da jerin rahotanni kan Sin da MDD da batun sauyin yanayi da samun ci gaba mai dorewa
2019-09-27 15:35:29        cri

Jiya Alhamis, tawagar Sin dake halartar babban taron MDD karo na 74 ta gabatar da rahotanni dangane da alakar Sin da MDD, da sauyin yanayi da samun ci gaba mai dorewa da sauransu.

Rahoto mai taken "Sin da MDD: takardar bayyana matsayin Sin a babban taron MDD karo na 74" ya bayyana gudunmawar da Sin take bayarwa ga MDD a fannoni 10 kan zaman lafiya da samun bunkasuwa da hakkin Bil Adama.

Ban da wannan kuma, rahoto mai taken "taron koli na MDD kan sauyin yanayi: Matsayi da matakan da Sin ta dauka", ya bayyana ra'ayin da Sin take dauka ta fuskar hadin kanta da kasashen duniya wajen tinkarar sauyin yanayi da kuma matakai da ci gaban da take samu a wannan fanni.

Dadin dadawa, rahoto mai taken "Ci gaban da Sin ta samu wajen gudanar da ajandar samun ci gaba mai dorewa na shekarar 2030", ya gabatar da matakai da ci gaba da Sin take samu, da kuma kalubale da take fuskanta da shirinta a nan gaba dangane da wannan rahoto, abin da ya bayyana sabon tunanin da Sin take bi da kuma niyyarta ta samun bunkasuwa mai inganci da ci gaban da take samu a wannan fanni.

Kazalika, rahoto mai taken "Manyan bayanai na kasa da kasa dake goyon bayan muradun samun ci gaba mai dorewa" ya bayyana kokarin da Sin take yi wajen marawa wadannan muradun baya ta hanyar amfani da wasu manyan bayanai, matakin da ya baiwa kasashen duniya cikakken bayani a wannan fanni, da ingiza tabbatar da ajandar samun muradun ci gaba masu dorewa na shekarar 2030. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China