Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sa kaimi ga raya dunkulewar Beijing da Tianjin da Hebei baki daya
2019-09-27 14:49:14        cri

Kakakin watsa labaru na ma'aikatar sufuri ta kasar Sin Sun Wenjian ya bayyana a jiya a nan birnin Beijing cewa, a halin yanzu, an samu nasarori kan ayyukan sufuri na dunkulewar Beijing da Tianjin da Hebei baki daya. A mataki na gaba kuma, za a raya tsarin sufuri na wurin, wanda zai shafi dukkan biranen dake yankin, ta hanyar jiragen kasa mafi sauri, da cimma burin rage tsawon lokacin sufuri a tsakanin birane dake makwabta zuwa kasa da awa daya da rabi.

A shekarun baya baya nan, an samu babban ci gaba kan tsarin raya sufuri a dunkulewar biranen Beijing da Tianjin da Hebei baki daya, ciki har da jiragen sama, da jiragen kasa, da tasoshin jiragen ruwa, da hanyoyin mota da sauransu. A gun taron manema labaru da aka gudanar a jiya, kakakin watsa labaru na ma'aikatar sufuri ta kasar Sin, Sun Wenjian ya yi bayanin cewa,  

"Na farko, an samu babban ci gaba kan ayyukan more rayuwa na sufuri. Ana kokarin gina manyan ayyukan sufuri ciki har da hanyoyin motoci cikin sauri a tsakanin Beijing da Qinhuangdao, Tianjin da Shijiazhuang da sauransu. Na biyu, an kafa tsarin hanyoyin jiragen kasa na matakin farko a yankin. An fara yin amfani da hanyoyin jiragen kasa a tsakanin tashar jiragen kasa dake yammacin Beijing da filin jiragen sama na Daxing, da gaggauta raya hanyoyin jiragen kasa mafi sauri a tsakanin Beijing da Shenyang, da tsakanin Datong da Zhangjiakou da saurasu. Na uku, ana cimma burin yin amfani da kati daya wajen yin zirga-zirga a dukkan biranen dake yankin."

A ranar 25 ga watan Satumba, aka fara amfani da filin jiragen sama na kasa da kasa na Daxing na Beijing, wanda ya samar da hidima ga fasinjoji da jigilar kayayyaki a yankin. A ranar 26 ga watan Satumba, aka fara amfani da hanyoyin jiragen kasa tsakanin yammacin Beijing da filin jiragen sama na Daxing. Bisa shirin da aka tsara, za a fara amfani da hanyoyin jiragen kasa tsakanin filin jiragen saman Daxing da Xiong'an a karshen shekarar 2020. Mataimakin shugaban ma'aikatar sufuri ta lardin Hebei Hou Zhimin ya bayyana cewa,

"Bisa shirin raya sufurin dunkulewar yankin, ya zuwa shekarar 2020, za a gama manyan ayyukan sufuri na yankin Xiong'an, da kafa tsarin tabbatar da sufuri na gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu. An sa kaimi ga raya dunkulewar sufurin yankin, sannan tsawon lokacin sufuri da za a kashe a tsakanin Xiong'an da Beijing zai tsaya kan rabin awa kacal."

A yayin raya dunkulewar yankin, birnin Tianjin yana kokarin gina yankin jigilar jiragen ruwa na kasa da kasa dake arewacin kasar Sin. A halin yanzu, akwai hanyoyin jiragen ruwa masu daukar kwantena 127, wadanda ke mu'amalar ciniki da tasoshin jiragen ruwa fiye da 500 na kasashen duniya fiye da 180.

Kakakin Sun Wenjian ya bayyana cewa, a halin yanzu, an shiga muhimmin lokacin raya dunkulewar Beijing da Tianjin da Hebei baki daya. Ma'aikatar sufuri ta kasar Sin za ta sa kaimi ga raya sufuri a wannan yanki da kuma yankin Xiong'an. Ya ce,  

"Na farko, a kafa tsarin sufuri na wuraren uku. Na biyu, a sa kaimi ga kyautata tsarin sufuri da magance gurbatar muhalli. Na uku, a tabbatar da sufurin cibiyar birnin Beijing ta biyu. Kuma na hudu, a yi kokarin kafa tsarin hanyoyin sufuri na yankin Xiong'an." (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China