Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsakaicin yawan kudin shigar Sinawa ya ninka wajen sau 60 a cikin shekaru 70 da suka wuce
2019-09-29 17:20:14        cri
A cikin shekaru 70 da suka gabata da kafa sabuwar kasar Sin, yawan kudin shiga da mazauna kasar suka samu ya samu saurin karuwa, inda a shekarar 2018, adadin ya kai RMB dubu 28 da doriya, wato ya ninka sau sama da 59 bisa na shekarar 1949. Sakamakon haka, Sinawa na kara jin dadin zaman rayuwarsu.

A cikin shekarun 70, zaman rayuwar Sinawa ya samu kyautatuwa sosai. Tun daga rashin ci gaba kan tattalin arziki da al'adu a farkon kafuwar sabuwar kasar Sin, zuwa kasancewa babbar kasa ta biyu a fannin tattalin arziki, jama'ar kasar Sin sun kafa tarihi a fannin tattalin arziki, ta yadda yawan kudin shiga da suka samu ya samu gagarumin sauyi.

A cikin shekarun 70 kuma, an samu kyautatuwa kan tsarin rarraba kudin shiga. Yawan kudin da mazauna kauyuka suka samu ya samu saurin karuwa, ana iya cewa, gibin dake kasancewa a tsakanin mutanen dake zama a birane da kauyuka na raguwa a fannin kudin shiga. An cimma nasarar taimakawa mutane sama da miliyan 700 wajen kawar da talauci.

Haka zalika, a cikin wadannan shekarun 70, karuwar kudin shiga ta kara karfin Sinawa wajen sayen kayayyaki, wanda ya kara ingancin zaman rayuwarsu.

An samu wannan babban ci gaba ne sakamakon kwazon da Sinawa ke da shi, da kuma ci gaba da wadata da kasar ta samu. A nan gaba, bisa karuwar ingancin tattalin arzikin kasar, yawan kudin shiga da Sinawa za su samu zai kara karuwa, haka zalika matsayin zaman rayuwarsu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China