Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An maido da huldar diflomasiya tsakanin kasar Sin da kasar Kiribati
2019-09-28 17:08:41        cri
A yau Asabar, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya sanar da labarin maido da dangantakar diflomasiya tsakanin kasar Sin da kasar Kiribati, inda ya ce lamarin ya nuna yadda ake rungumar manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.

Kakakin ya ce, a jiya Jumma'a ne mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, da shugaban kasar Kiribati, kana ministan harkokin wajen kasar, Taneti Mamau, suka sa hannu kan hadaddiyar sanarwar maido da dangantaka tsakanin kasashen 2, a birnin New York na Amurka.

Mista Geng ya kara da cewa, Kasar Sin daya tak ce a duniya, kana gwamnatin jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, ita ce gwamnati daya tilo dake wakiltar daukacin al'ummun Sinawa, yayin da Taiwan wani bangare ne na yankin kasar Sin, wanda ba za a yarda ya balle ba. Wannan batu, a cewar kakakin, wani ra'ayi ne na bai daya ga gamayyar kasa da kasa. Saboda haka yadda gwamnatin kasar Kiribati ta yanke hulda da Taiwan, gami da maido da dangantakar diflomasiya da jamhuriyar jama'ar kasar Sin, mataki ne da ya dace da yanayin duniya, da kuma ra'ayin jama'a. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China