Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan ta'addan BH sun tsere daga maboyarsu biyo bayan hararen soji
2019-09-20 09:14:10        cri

Rundunar sojin Nijeriya ta ce 'yan ta'addan BH sun tsere daga maboyarsu a yankin tafkin Chadi, zuwa yankunan arewa da tsakiyar nahiyar Afrika, yayin da sojojin kawancen kasashen yankin ke tsaka da kai musu hari.


Wata sanarwa da kakakin rundunar Sagir Musa ya fitar, ta ce hare-haren da sojojin rundunar da na kawancen kasashen ke kai wai maboyar 'yan ta'ddan ne ya sanya su tsarewa.


Ya kara da cewa, akwai sahihan rahotanni dake nuna cewa 'yan ta'addan na barin yankin, inda ya alakanta hakan da luguden wuta ta sama da kasa da sojojin kawancen ke kai wa, wanda kuma ya yi sanadin kashe 'yan ta'addan da ba a san adadinsu ba tare da lalata makamansu.
Kakakin ya ce dakarun kasar da na kawancen, za su ci gaba da sintiri da hana 'yan ta'addan da suka tsere, daga sake komawa yankin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China