Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da takardar bayani kan Sin da alakarta da sassan duniya a sabon karni
2019-09-27 14:48:56        cri
Albarkacin cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ta ba da wata takardar bayani kan Sin da alakarta da sauran sassan duniya a sabon karnin da muke ciki a yau Juma'a, wadda ta yi cikakken bayani kan ci gaban da Sin take samu, da hanya da alkiblar da Sin take bi da yin tsokaci kan dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen duniya. Ta yadda kasashen duniya za su kara fahimtar bunkasuwar kasar Sin.

Takardar ta nuna cewa, Sin ta kwashe shekaru kasa da dari daya wajen samun bunkasuwa, wanda ya dauki kasashe masu wadata shekaru fiye da dari kafin su cimma, inda har GDPn kasar ya kai matsayi na biyu a duniya. Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 sun fito daga mawuyancin hali na karancin kayayyaki, har sun shiga cikin wadata da rayuwa cikin mutunci da ba a taba ganin irinta ba a tarihi.

Ban da wannan kuma, takardar ta ce, a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, Sin ta samu bunkasuwa sosai, a sa'i daya kuma ta ba da gudunmawarta yadda ya kamata ga zaman lafiyar duniya da karfafawa sauran kasashe wajen samun bunkasuwa tare.

Dadin dadawa, jagorancin JKS ya zama muhimmin mataki na samun bunkasuwar kasar Sin, Sinawa na bullo da hanyar da ta dace da suke bi wajen samun bunkasuwa, wato hanyar tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, hanya ce da Sin za ta ci gaba da kamawa nan gaba.

Game da bunkasuwar kasar Sin da kasashen duniya suke mai da hankali kansa, takardar ta jaddada cewa, bunkasuwar Sin yana kunshe da damammaki masu kyau ga duniya, a maimakon kalubale da barazana. Ta kara da cewa, Sin ta kasance babban karfi dake ba da tabbaci ga bunkasuwar duniya gaba daya, manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje da Sin ta dade tana aiwatarwa ta samar da damammaki masu inganci ga kasashen duniya, kazalika, Sin ta samarwa kasashen duniya karin kayayyakin more rayuwa. Bunkasuwar kasar Sin na samarwa sauran kasashe fasahohi da abin koyi masu kyau, kuma Sin ba za ta kama hanyar kama karya ba har abada. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China