Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a binne marigayi Mugabe a makabartar karrama 'yan mazan jiya dake Harare
2019-09-13 19:45:58        cri
Mai magana da yawun iyalin tsohon shugaban kasar Zimbabwe, kuma dan uwa ga marigayin Mr. Leo Mugabe, ya ce za a binne marigayi Robert Mugabe a makabartar karrama 'yan mazan jiya dake birnin Harare, a wani lokaci da za a bayyana nan gaba.

Leo Mugabe ya shaidawa 'yan jarida hakan a Juma'ar nan, cewa za a dauko gawar baffan na sa zuwa makabartar ne a ranar Lahadi, bayan kammala dukkanin hidindimun karrama gawar, kamar harba bindigogi 21, da gabatar da babbar lambar yabo ta gwarzon kasar ga marigayin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China