Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An isar da gawar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Mugabe birnin Harare
2019-09-12 10:59:56        cri

Jirgin sama na musamman mai dauke da gawar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya isa birnin Harare, babban birnin kasar Zimbabwe da yammacin ranar 11 ga wata. Shugaban kasar na yanzu Emmerson Mnangagwa da manyan jami'an gwamnatin kasar da kuma jama'a fiye da dubu daya sun isa filin jiragen saman kasar domin maraba da saukar gawar marigayin.

Shugaba Mnangagwa ya yi jawabi a filin jiragen saman, inda ya nuna yabo ga dukkan rayuwar Mugabe, ya ce Mugabe muhimmin shugaban kasar ne, da ya jagoranci juyin juya hali, kuma mai bin ra'ayin neman daidaiton bakakken fata.

Game da shirin ta'aziyya, gwamnatin kasar Zimbabwe za ta yi taron makokin Mugabe a babban filin wasa na kasar a ranar 14 ga wannan wata. Kuma za a binne gawarsa a ranar 15 ga wata.

Mugabe ya rasu a wani asibitin dake kasar Singapore a ranar 6 ga wannan wata, yana da shekarun haihuwa 95. A wannan rana, gwamnatin kasar Zimbabwe ta nada masa sunan "jarumin kasar Zimbabwe", an kuma sanar da fara juyayi a dukkan kasar har zuwa ranar taron makoki. Har yanzu, gwamnatin kasar ba ta gabatar da wurin binne shi ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China