Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu sojojin Senegal 3 sun mutu sakamakon hadarin jirgin sama a CAR
2019-09-28 16:53:19        cri
Wasu sojojin wanzar da zaman lafiya 3, 'yan kasar Senegal, sun rasa rayukansu, yayin da daya ya samu rauni, sakamakon faduwar wani jirgin sama mai saukar ungulu samfurin Mi-24 a kasar Afirka ta Tsakiya CAR a jiya Jumma'a.

Stephane Dujarric, kakakin babban magatakardan MDD Antonio Guterres ne ya sanar da lamarin, inda ya ce jirgin ya fadi ne yayin da yake kokarin sauka cikin gaggawa, sakamakon yanayi maras kyau da aka gamu da shi, a wani wurin dake dab da Bouar na yammacin kasar CAR.

A cewar kakakin, ana amfani da jirgin saman ne wajen tallafawa aikin dakile wata kungiyar masu tada zaune-tsaye a gundumar Nana-Mambere ta kasar.

Stephane Dujarric ya ce, babban magakatardan da Majalisar, sun yi wa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu ta'aziyya, gami da jajantawa gwamnati da al'ummar kasar Senegal.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China