Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yabawa dangantakar Sin da Afrika wajen inganta zaman lafiya
2019-09-27 10:12:32        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yabawa dangantakar Sin da kasashen Afrika, wanda ke kara habaka.

Cikin sakon da ya aike ga taron ministoci kan dangantakar Sin da Afrika game da batutuwan dake gaban kwamitin sulhu na majalisar, Antonio Guterres, ya ce dangantakar Sin da Afrika domin inganta zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar na kara habaka cikin sauri, kuma ta hanyoyi mabanbanta, cikin sama da shekaru 10 da suka gabata.

Ya ce kyautatuwar dangantakar bangarorin biyu na zuwa ne a lokacin da kasashen Afrika ke kokarin kara karfinsu na wanzar da zaman lafiya ta kowacce fuska, daga daukar matakan kariya, zuwa na wanzar da zaman lafiya, karkashin ci yunkurin samun ci gaba mai dorewa na bai daya.

Sakatare Janar din ya kara da cewa, Sin da MDD ma na hada hannu kan wasu batutuwan dake gaban kwamitin sulhu na majalisar.

Har ila yau, ya ce MDD na hada hannu da Tarayyar Afrika da sauran kungiyoyin nahiyar kan kokarin shiga tsakani a kasashen Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Madagascar da Sudan da Sudan ta Kudu da kuma Guinea-Bissau.

Ya kuma bada misali da kasar Mali, inda ake da jami'an soji Sinawa 421 dake aiki karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar wato MINUSMA, wanda ya kasance daya daga cikin shirye-shiryen majalisar mafi fuskantar kalubale. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China