Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kamfanonin Inshora a nahiyar Afrika su rungumi hanyoyin fasaha don raya bangaren
2019-09-20 11:09:16        cri
Kamfanin inshorar kamfanonin Inshora na Afrika ZEP-RE, ya yi kira ga kamfanonin inshora na nahiyar, su rungumi hanyoyin fasaha da kuma taimakawa wajen fadada samar da hidimomin inshora.

Manajan Daraktan kamfanin ZEP-RE, Hope Murera, ta ce bangaren inshora ya cancanci a kirkiro masa da sabbin abubuwa, kuma lokaci ya yi da ya kamata a rungumi tsarin fasaha domin kara inganta bangaren.

Ta ce bangaren inshora ne ya zama koma baya wajen rungumar fasaha a duniya, idan aka kwatanta da sauran bangarorin hada-hadar kudi, lamarin da ya zaburar da kamfanin ZEP-RE wajen yayata batun kirkiro sabbin abubuwa a bangaren ta hanyar shirya taruka, tana mai cewa bangaren na fuskantar sauye-sauye a duniya baki daya.

Manufar taron ita ce, gabatar da bukatar kamfanonin inshora su hada hannu wajen samar da fasahar da za ta sauya bangaren domin kara masa inganci da kuma bunkasa shi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China