Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron tattaunawa kan zuba jari ga Afirka karo na 5
2019-09-12 10:50:14        cri
An bude taron tattaunawa kan zuba jari ga Afirka karo na 5 a birnin Brazzaville dake kasar Congo Brazzaville a ranar 10 ga wata, takensa a wannan karo shi ne "kara yin hadin gwiwa don sa kaimi ga samar da ayyukan yi da raya tattalin arziki a fannoni daban daban a Afirka", inda masu halarta suka tattauna batutuwan dake shafar taken taron.

Shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou Nguesso ya yi jawabi a gun bikin budewar yana cewa, kasashen Afirka suna fuskantar damar samun bunkasuwa, kuma ya kamata a raya dangantakar hadin gwiwa mai kyau a tsakaninsu da sauran kasashen duniya ciki har da kasar Sin don samun moriyar juna.

Shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki ya yi nuni da cewa, kafuwar yankin yin ciniki cikin 'yanci na Afirka zai jawo kamfanonin kasashen waje su zuba jari ga Afirka, kana kasashen Afirka za su kara inganta dangantakar hadin gwiwa a tsakaninsu da sauran kasashen duniya don sa kaimi ga samar da ayyukan yi, da bunkasuwar tattalin arziki, da kuma cimma burin ajendar shekarar 2063 da kungiyar AU ta tsara.

Mataimakin shugaban bankin raya kasa na kasar Sin Liu Jin ya yi jawabi, inda ya ce, ya kamata Sin da Afirka su nemi hanyoyin zuba jari da tattara kudi masu dacewa don nuna goyon baya ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China