Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shigar da jirgin ruwan dakun kwatena mai amfani da karfin gas na farko a duniya da Sin ta kera a cikin ruwa
2019-09-26 13:42:40        cri
An shigar da jirgin ruwan dakun kwatenoni mai amfani da karfin gas na farko a duniya wanda Sin ta kera a cikin ruwa a birnin Shanghai dake kasar Sin a jiya, wannan ne jirgin ruwa na farko a duniya mai amfani da irin wannan karfin gas, wanda kuma ke iya daukar kwantenoni 23000.

Tsawon jirgin ruwa ya kai mita 400, fadinsa ya kai mita 61.3, sannan fadin shimfadadden karfe na jirgin ruwa ya kai kimanin na filayen wasan kwallon kafa guda 4. Nauyin kayayyakin da jirgin ruwan zai iya dauka ya kai ton dubu 220, yawan kwatena da zai iya dauka ya kai 23000, wanda shi ne mafi girma bisa na sauran jiragen ruwa. Yawan iskar Carbon Dioxide da yake fitarwa ya ragu da kashi 20 cikin dari, sannan yawan iskar dunkulen sinadaran nitrogen oxides da yake fitarwa ya ragu da kashi 85 cikin dari.

Za a fara yin amfani da jirgin ruwan a hukunce a watan Afrilun shekarar 2020. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China