Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a tsaya tsayin daka kan manufar samun bunkasuwa cikin lumana da samun moriyar juna ta hadin gwiwa
2019-09-26 09:24:26        cri
Kasar Sin ta riga ta kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninta da kasashe fiye da 170 na duniya, da shiga manyan kungiyoyin kasa da kasa, da kuma raya dangantakar abota a tsakaninta da kasashen duniya 109.

An ce, idan manufa ta dace, za a kara samu magoya baya. Sabuwar kasar Sin ta samu nasarori a kan harkokin waje domin ta tsaya tsayin daka kan manufar samun bunkasuwa cikin lumana da samun moriyar juna ta hadin gwiwa. Sin ta gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", wadda kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 160 suka goya mata baya domin an yi shawarar bisa ka'idar adalci da samun moriyar juna. Idan aka kauracewar manufar kama karya, to za a kara samun abokai na hakika. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China