![]() |
|
2019-09-25 14:39:28 cri |
Za a gudanar da bikin faretin soja na murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a ranar 1 ga watan Oktoban bana a nan birnin Beijing. A Talata ne, mataimakin shugaban ofishin bada jagorancin ayyukan bikin, Manjo Janar Cai Zhijun ya bayyana wa 'yan jarida cewa, bikin faretin soja a wannan karo ya kasu zuwa matakai biyu, wato na farko, shugaban kasar zai duba sojojin da za su halarci bikin, sa'an nan kuma sojojin a cikin rukuni-rukuni za su yi yawo a filin Tian'anmen. Za a shafe tsawon minti 80 ana bikin, kuma bikin a wannan karo zai kasance mai kasaita da zai fi na shekarun baya bayan nan. Cai Zhijun ya bayyana cewa,
"Sojojin da za su halarci bikin faretin za su tsaya a titin Chang'an, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping zai duba faretinsu. Daga baya, sojojin a cikin rukuni-rukuni za su ratsa filin Tian'anmen suna tafiya suna fareti. Yawan sojoji a cikin rukunoni 59 da tawagar sojojin buga kida ta hadin gwiwa da za su halarci bikin faretin soja a wannan karo ya kai kumanin dubu 15, yawan jiragen saman kuma ya kai fiye da 160, a yayin da yawan makaman da za a gwada zai kai 580, girman bikin zai fi na lokacin baya."
Bikin faretin soja da za a gudanar nan ba da jimawa ba, zai zama karo na farko, tun bayan da kasar Sin ta shiga sabon yanayin da take ciki, kuma makasudinsa shi ne shaida niyyar sojojin kasar Sin na tabbatar da ikon kasa, da tsaro, da moriyar bunkasuwa, da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Manjo Janar Cai Zhijun ya yi bayanin cewa, akwai abubuwa masu yawa na a zo a gani a bikin da za a gudanar, wasu rukunonin sojojin da dama za su halarci bikin a karo na farko, kana yawan sabbin makaman da za a gwada a wannan karo sun yi yawa. Ya ce,
"Bisa kwaskwarimar da aka yi na gina tsarin aikin soja na zamani mai sigar musamman ta kasar Sin, wasu rukunonin soji za su halarci bikin faretin soja na wannan karo a karon farko. Kana yawan sabbin makaman da za a gwada, za su dauki wani babban kashi na jimilar makaman da za a gwada a bikin. Ban da wannan kuma, rukunin sojojin kiyaye zaman lafiya za su halarci bikin a wannan karo, wanda ya shaida niyyar sojojin kasar Sin ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya."
Cai Zhijun ya kara da cewa, a halin yanzu, bayan da aka yi kwaskwarima kan tsarin sojojin kasar Sin, an shiga sabon lokacin gudanar da ayyukan soja cikin hadin gwiwa a tsakanin sojoji daban daban don inganta karfin aikin soja na hadin gwiwa, kuma wannan muhimmin aiki ne na yin kwaskwarima da raya sojojin kasar Sin. A gun bikin faretin soja a wannan karo, za a gwada tunanin yin hadin gwiwa a mataki daban daban.
A gun bikin faretin soja na bana, za a gwada sojojin kasar bayan da aka yi kwaskwarima kan tsarin aikin soja a dukkan fannoni, za a gwada wasu sabbin makaman zamani karo na farko, don nuna karfin kasar ta Sin wajen yin kirkire-kirkire da sadarwa na kiyaye tsaron kasar. Mataimakin shugaban ofishin bada jagorancin ga ayyukan bikin faretin soja Tian Min ya yi bayani cewa,
"Na farko, dukkan makaman soja da za a gwada a bikin kirar kasar Sin ne da ake amfani da su a yanzu, ciki har da wasu sabbin makamai, wadanda ya shaida tsarin makaman sojojin kasar Sin, tare da karfin yin kirkire-kirkire ta fannin kiyaye tsaron kasar. Na biyu, yawancin makaman da za a gwada suna amfani da fasahohin sadarwa na zamani. Wannan ya shaida cewa, za a inganta ingancin ayyukan makaman." (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China