Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenneth David Kaunda: Zambiya da Sin, aminai ne a ko da yaushe
2019-09-16 14:33:56        cri

Bana, shekaru 55 ke nan da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen Zambiya da Sin kana shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Kenneth David Kaunda mai shekaru 95 da haihuwa ya jinjina wa dankon zumunci da ke tsakanin kasashen Zambiya da Sin matuka. A cewarsa, amincinsu na da matukar muhimmanci.

Yayin da mista Kaunda yake zantawa da wakiliyarmu, tsohon shugaban na Zambiya da ya kafa kasar kuma wanda ya sa hannu a aikin ayyukan kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2 ya bayyana cewa, amini ne a ko da yaushe a zumuncin da ke tsakanin kasashen 2.

Mista Kaunda ya ga wasu muhimman lokuta a tarihin kasashen na Zambiya da Sin da kuma ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen 2.

A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1964, lokacin da Zambiya ta samu 'yancin kanta, kashegari kuma ta sanar da kulla huldar jakadanci da Sin.

Mista Kaunda ya bayyana cikin jawabin da ya gabatar a MDD cewa, ba daidai ba ne a ce babu wakilin jamhuriyar jama'ar kasar Sin a MDD. Ya ba da gudummowarsa wajen maido da kujerar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a MDD.

Mista Kaunda ya mulki Zambiya a matsayin shugaban kasa daga watan Oktoban shekarar 1964 zuwa watan Nuwamban shekarar 1991.

A shekarar 1967, mistan Kaunda ya kawo ziyarar aiki kasar Sin a karo na farko, inda ya gana da shugabannin kasar Sin.

Mai shekaru 95 da haihuwa, Kaunda ya bayyana cewa, a wancan lokaci, kasar Sin ita ma tana fama da matsalar tattalin arziki, amma duk da haka, marigayi shugaba Mao Zedong ya tsai da kudurin ba da taimakon shimfida hanyar dogo a tsakanin Tanzaniya da Zambiya, ta yadda kasashen 2 za su kare 'yancin da suka samu da kuma yaki da 'yan mulkin mallaka da masu nuna wariyar al'umma. Kasashen 2 da ma nahiyar Afirka, sun bayyana hanyar dogon da ke tsakanin Tanzaniya da Zambiya, wadda ta kasance kamar mafarin sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka, a matsayin hanyar neman 'yanci da sada zumunta.

Bayan da Kaunda ya dawo gida, a karo na farko ya bayyana kasar Sin a matsayin aminiyar Zambiya a ko da yaushe. Daga nan kuma, wurare da dama suka fara bayyana huldar da ke tsakanin Sin da Zambiya da kuma huldar da ke tsakanin Sin da Afirka a matsayin aminai a ko da yaushe.

A cewar tsohon shugaban Zambiya, zumuncin da ke tsakanin Zambiya da Sin, sakamako ne da jama'ar kasashen 2 suka samu ta hanyar yin gwagwarmaya tare. Abokanmu na Sin sun ba mu babban taimako a fannonin kiwon lafiya, raya ababen more rayuwar jama'a da dai sauransu. Mun gode musu sosai. Muna fatan karin jama'ar Sin za su kafa kasarmu ta Zambiya cikin hadin gwiwa da jama'ar Zambiya.

Ko bayan da mista Kaunda ya yi murabus daga mukaninsa na shugaban kasa, kuma ya tsofa sosai, amma kamar yadda ya yi a baya, yana mai da hankali kan ci gaban huldar da ke tsakanin kasarsa da Sin. Ya kan halarci wasu harkokin inganta huldar da ke tsakanin kasashen 2.

A ranar 13 ga watan Mayun bana, an yi bikin kaddamar da gina wurin tunawa da shimfida hanyar dogo a tsakanin Tanzaniya da Zambiya a Zambiya. Ko da yake ba shi da koshin lafiya, amma Kaunda ya halarci bikin tare har ma ya yi jawabi. A cewarsa, jama'ar Zambiya ba za su manta da gudumowar tsawon shekaru da jama'ar Sin suka bayar ba tare da son kai ba. Wurin tunawa da shimfida hanyar dogo a tsakanin Tanzaniya da Zambiya a Zambiya zai kasance wata alamar yin hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Zambiya, wanda kuma zai sa jama'a su rika tunawa da lamarin.

A ko da yaushe abokan kasar Sin suna ziyartar Zambiya, mista Kaunda da kansa ya kan yi musu maraba, muddin yana da koshin lafiya. Ya kan goge goshin ko wane bako da farin hankicinsa, ya nuna musu fatan alheri, tare da yin hira da abokan kasar Sin dangane da abokantakar da ke tsakanin kasashen 2.

A cewar mista Kaunda, jama'ar kasashen Zambiya da Sin har yanzu muna raya sahihiyar abokantaka da kyakkyawar hadin gwiwa. Muna da tarihi kusan irin daya. Mu 'yan uwa ne, kuma mu aminai ne a ko da yaushe. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China