Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta raba ma sauran kasashe fasahohinta na tinkarar kwararar hamada
2019-09-12 13:33:52        cri

 

Tun daga ranar 2 har zuwa ranar 13 ga watan da muke ciki, an gudanar da taro na 14 na bangarorin da suka sa hannu kan yarjejeniyar hana kwararar hamada ta MDD ko (UNCCD) a New Delhi na kasar Indiya, inda tawagar kasar Sin ta raba fasahohinta a fannin tinkarar kwararar hamada ga sauran kasashe.

A shekarun baya, kasar Sin ta samu fasahohi sosai a fannonin hana kwararar hamada, gami da kare kasa daga zaizaya, har ma ta yi amfani da fasahohin wajen fitar da dimbin mutane daga kangin talauci, ta yadda ta samu yabo sosai daga gamayyar kasa da kasa. Saboda wannan yanayin da take ciki ne, kasar Sin ta kira wani taron ministoci a gefen taron UNCCD na wannan karo mai taken " karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, don samar da alheri ga jama'a" a birnin New Delhi a ranar 8 a watan da muke ciki, inda aka samu wakilai fiye da 100 masu wakiltar kasasahe da kungiyoyi kimanin 30 da suka halarci taron.

Yayin taron, shugaban tawagar kasar Sin, kuma darektan hukumar itatuwa da filayen ciyayi ta kasar mista Zhang Jianlong, ya bayyana cewa, babu wata kasa da za ta iya daidaita matsalar kwararar hamada ita kadai, domin ana bukatar hadin gwiwa a wannan fanni. Saboda haka, an mai da aikin dakile kwararowar hamada, da kokarin kare kasa don magance zaizayarta, a matsayin wani muhimmin fannin da ake gudanar da hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa, yayin da kasar ta Sin har kullum ke kokarin raya huldar hadin kai tare da sauran kasashe masu tasowa.

A wajen wannan taro, an cimma ra'ayi daya kan yadda za a gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa don tinkarar kwararar hamada, inda aka jaddada bukatar yada ra'ayin kare muhalli, da gina wata al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, inda ake samun muhalli mai kyau, da sana'o'i masu ci gaba, gami da tattalin arziki mai inganci.

Sa'an nan a nasa bangare, sakataren zartaswa na sakatariyar UNCCD Ibrahim Thiaw, ya yaba wa kasar Sin kan ci gaban da ta samu a fannin tinkarar kwararar hamada, kana ya bayyana niyyarsa ta rufa wa kasar Sin baya, a kokarinta na hadin gwiwa tare da sauran kasashe masu tasowa.

Daga bisani, a ranar 9 ga watan Satumban da muke ciki, an gayyaci shugaban kamfanin ELION na kasar Sin mista Wang Wenbiao, wanda ya samu wata babbar lambar yabo daga MDD bisa dalilin jagorantar aikin dakile kwararar hamada a yankin hamadar Kubuqi ta kasar Sin, domin ya bayyana fasahohin da ya samu a fannin tinkarar kwararowar hamada.

Fadin hamadar Kubuqi ya kai muraba'in kilomita dubu 18.6. Amma bayan da aka kwashe shekaru 30 ana kokarin daidaita wannan wuri, yanzu an mai da hamadar mai fadin muraba'in kilomita fiye da 6000 ta zama filin ciyayi. A lokaci guda, kudin shiga na mutanen wurin ya karu daga Yuan 400 zuwa fiye da Yuan dubu 10, bisa kokarin kyautata muhallin da suke zama a ciki.

A cewar mista Wang Wenbiao, wani babban ci gaba da aka samu a kokarin tinkarar kwararar hamadar Kubuqi shi ne, samun amsa ga wasu tambayoyin da a kan yi yayin kula da hamada, wato " Ta yaya za a daidaita muhalli? Daga ina za a samu kudin da ake bukata? Ta yaya za a tabbatar da samun riba daga aikin? " da kuma, " Ta yaya za a tabbatar da dorewar aikin?" Mista Wang ya ce, yana so ya yayata fasahohi masu ci gaba da aka samu ga sauran kasashe masu fama da matsalar kwararar hamada. Yana kuma neman ganin hadin gwiwar daukacin bil Adama, a kokarin tinkarar sauyawar yanayin duniya.

Yayin da Ibrahim Thiaw, sakataren zartaswa na sakatariyar UNCCD ke hira da manema labaru, ya ce shi ma an haife shi a wani yanki dake da hamada, don haka ya fahimci matsalar da kwararar hamada ke haifarwa zaman rayuwar jama'a. A cewarsa babbar nasarar da aka samu a kokarin dakile kwararar hamada a Kubuqi tana ba mutane mamaki, kuma shi ne lamarin daidaita hamada mafi ci gaba da ya taba gani a duniya.(Bello Wang)


 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China