Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan malaman kasar Sin ya karu da kashi 80 cikin dari a cikin shekaru 35 da suka gabata
2019-09-10 14:14:00        cri

Yau ranar 10 ga watan Satumba, ita ce ranar malamai ta kasar Sin ta 35. Bisa alkaluman kididdigar da ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta gabatar, an ce, bayan da aka kafa ranar malamai ta kasar Sin, yawan malaman kasar ya karu da kashi 80 cikin dari. Musamman bayan taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, inda yawan malaman kasar ya karu sosai, kana yawan albashin malaman kasar ya karu da dama, wanda ya kai matsayi na 7 bisa manyan sana'o'i 19 na kasar.

Malam Fei Haimin yana aikin koyarwa a wata makarantar yankin Mongoliya cikin gida har na tsawon shekaru fiye da 30. Ya bayyana cewa, a shekarun baya baya nan, an gina wuraren zaman malamai, da ginin wuraren koyarwa, da ginin wuraren cin abinci, da wurin zama na dalibai, wanda hakan ya kyautata sharuddan karatu na dalibai, da kuma yanayin rayuwa na malamai. Malam Fei ya bayyana cewa,

"An kyautata yanayin aiki da rayuwar, kana yawan albashinmu na karuwa shekara bayan shekara, kana an riga an ba da kudin rangwame ga malamai masu aiki a yankuna masu fama da talauci."

Bisa alkaluman kididdigar da ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta gabatar, yawan malaman kasar a halin yanzu ya kai miliyan 16 da dubu 738 da dari 3, adadin da ya karu da kashi 80 cikin dari bisa na shekarar 1985, wato lokacin da aka kafa ranar malamai ta kasar Sin. A fannin matsayin karatun malamai kuwa, yawan malamai masu aiki a makarantun firamare da suka samu digirin farko na jami'a ya karu da kashi 61.59 cikin dari bisa na shekarar 1985, kana yawansu a makarantun midil ya karu da kashi 80.59 cikin dari. Haka kuma, yawan albashin malamai bai wuce matsayi na uku na karshen sana'o'in kasar Sin kafin shekarun 1980 na karnin da ya gabata ba, amma a halin yanzu, yawansa ya kai matsayi na 7 na manyan sana'o'i 19 a kasar Sin.

Mataimakin shugaban sashen kula da kimiyya da fasaha, da ba da ilmi da al'adu na ma'aikatar kudi ta kasar Sin Lv Jianping ya yi bayani cewa, a wasu shekarun da suka gabata, ma'aikatar kudi ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kara mai da hankali kan malamai, inda yawan albashin malamai ya samu karin fiye da kaso 50 cikin dari bisa dukkan kudin da aka kashe a fannin ba da ilmi. Malam Lv ya bayyana cewa,  

"Ya kamata a kara zuba jari ga raya ayyukan kula da malamai. Hukumomin kudi sun tsaya tsayin daka kan manufar raya aikin ba da ilmi da farko, da kara zuba jari ga wannan fanni. Tun daga shekarar 2013 zuwa 2018, yawan kudin da aka kashe a fannin ba da ilmi a kasar Sin ya kai Yuan biliyan dubu 16 da 200, kwatankwacin yawansu kuma ya karu da kashi 7.9 cikin dari a kowace shekara."

Shirin tura malamai zuwa yankuna na musamman, manufar musamman ce da hukumomin ba da ilmi na kasar Sin suka aiwatar, domin raya sha'anin ba da ilmi na yankin yammacin kasar. Ana neman masu kammala karatu daga jami'a, ana tura su zuwa kauyukan yankunan yammacin kasar, don warware matsalolin rashin samun malamai a kauyukan dake yankunan. Lv Jianping ya ce, hukumomin ba da ilmi na kasar Sin sun kara kyautata tsarin albarkatun malamai, da kara sa lura ga malamai masu aiki a kauyuka. Ya ce,  

"Ana ba da kudin rangwame ga malamai masu aiki a yankunan musamman. Tun daga ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2018, yawan albashin malamai masu aiki a yankunan yammacin kasar ya karu zuwa Yuan dubu 38.2 a kowace shekara, kana yawan albashin su a yankunan tsakiyar kasar ya karu zuwa Yuan dubu 35.2 a kowace shekara. A shekarar 2019, yawan malamai da aka samu daga shirin tura malamai zuwa yankuna na musamman ya kai dubu 100, kana hukumomin kudi sun zuba jari da ya kai Yuan biliyan 43 a wannan fanni tsakanin shekarar 2013 zuwa 2019." (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China