Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan magance ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi na yankin Xinjiang su ne gudummawar da Sin ta samarwa sha'anin yaki da ta'addanci na duniya
2019-09-26 10:39:10        cri
A jiya ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya halarci taron hadin gwiwar yaki da ta'addanci na kwamitin sulhun MDD da kungiyoyin yankuna a cibiyar MDD dake birnin New York na kasar Amurka.

A cikin jawabinsa, Wang Yi ya yi bayani game da matakan magance ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi da aka dauka a yankin Xinjiang na kasar Sin, inda ya jaddada cewa, gwamnatin yankin ta dauki matakan da suka dace, da koyi da fasahohi daga sauran kasashe don aiwatar da ayyukan magance ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi bisa dokoki, yana mai cewa, ta hakan aka magance karin faruwar ayyukan ta'addanci, kuma jama'ar kasar Sin ciki har da 'yan kabilu daban daban dake yankin Xinjiang sun goyi bayan matakan, wadanda su ne gudummawar da kasar Sin ta samarwa sha'anin yaki da ta'addanci na duniya. Kuma mutanen kasashen waje da suka taba ziyarta yankin Xinjiang sun amince da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, wasu kasashen yammacin duniya ciki har da kasar Amurka sun yi biris da hakikanin yanayi, da zargi kasar Sin ba bisa tushe ba domin yunkurinsu na siyasa, yana mai cewa Sin, har ma da kasa da kasa sun ki amincewa da su. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China