Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kasance kasa dake cikakken tsaro a duniya
2019-09-24 16:27:54        cri

Kasar Sin ta yanzu ta kafa tsarin dokoki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin bisa tsarin mulkin kasar dake shafar dukkan fannoni. Ana tafiyar da dokoki da matakai na shari'a kamar yadda aka tsara yadda ya kamata, da watsa yadda ake yanke hukunci ta internet kai tsaye da sauransu. Sin ta tsaya tsayin daka kan yaki da laifuffuka bisa dokoki, a 'yan shekarun nan, adadin Sinawa dake aikata laifuffukan kisa ya yi kasa da kaso 1 cikin dubu 100 a shekara, Sin tana daya daga cikin kasashe dake cikakken tsaro a duniya.

Yadda kasar ke tafiyar da harkoki bisa dokoki ita ce hanya mafi muhimmanci wajen samun zaman lafiya a kasar. Ana gudanar da ayyukan kasar a fannoni daban daban bisa dokoki. Yanzu ana cimma daidaito kan kafa dokoki masu dacewa, da gudanar da ayyuka bisa dokoki a cikin adalci, da yadda jama'a za su martaba dokoki a dukkan zamantakewar al'ummar kasar. Sin tana tafiyar da harkokin kasa bisa dokoki, da kare dukkan halatattun moriyar 'yan kasuwa na kasashen waje, da yanke hukunci ga dukkan masu aikata laifuffuka, don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin al'umma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China