Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara amfani da filin jiragen sama na kasa da kasa na yankin Daxing na Beijing
2019-09-25 14:27:25        cri

Yau Laraba, aka fara amfani da filin jiragen saman kasa da kasa na yankin Daxing dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Nan gaba, filin jiragen sama na kasa da kasa na yankin Daxing, da filin jiragen sama na kasa da kasa na babban birnin kasar, za su ba da gudummawa wajen kyautata yanayin sufurin kasar Sin, wadanda za su samar da sauki kan aikin sufurin jiragen sama dake tsakanin kasa da kasa.

Filin jiragen sama na Daxing ya ratsa yankin Daxing na birnin Beijing da birnin Langfang na lardin Hebei, wanda aka zuba jarin yuan biliyan 450, zai kuma iya jigilar fasinjoji zuwa yankuna 112.

Bisa labarin da aka samu, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai kamfanonin jirga-jirgar jiragen sama na kasar Sin guda 7, da kuma kamfanonin jirga-jirgar jiragen sama na kasashen waje guda 8 da za su shiga filin jiragen sama na Daxing dake birnin Beijing. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China