Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala aikin gina sabon filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Beijing
2019-07-01 11:36:55        cri

A jiya ne aka kammala aikin gina filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Beijing Daxing na kasar Sin, kuma an fara shirye-shiryen fara aiki da filin jiragen saman da ake ganin zai kasance mafi hada-hadar jiragen sama a duniya.

A cikin watanni shida na farkon shekara, an yi nasarar kammala ayyukan da suka hada da, filin jiragen saman kansa, da sashen kula da tashi da saukar jiragen sama, da na'urorin shan mai na jiragen sama da manyan hanyoyin da suka hade filin da jirgin kasa mai saurin tafiya a kan lokaci, an kuma ba da iznin fara aiki da su.

Filin tashi da saukar jiragen sama na Beijing Daxing wanda aka shirya zai fara aiki kafin ranar 30 ga watan Satumban wannan shekara, zai kasance cibiyar hada-hadar jiragen sama mai muhimmanci ga masu tafiye-tafiye na kasa zuwa kasar Sin da ma masu fita daga kasar, matakin da zai taimakawa ci gaban kasar Sin, zuwa kasuwar hada-hadar jiragen sama mafi girma a duniya da ake hasashen da za ta kasance nan da tsakiyar shekarun 2020.

Ana kuma yi hasashen cewa, sabon filin jirgaren saman, zai karbi fasinjoji da za su kai miliyan 72 a shekarar 2025, za kuma karu zuwa miliyan 100 nan da shekarar 2040. Ana kuma yi hasashen filin jirgin saman na Beijing Daxing zai dara filin tashi da saukar jiragen sama na Hartsfield-Jackson Atlanta na kasa da kasa dake Amurka, wajen zama filin jirgin sama mafi karbar fasinjoji a duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China