Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing ya samu mahalarta sama da miliyan 1.8
2019-06-04 11:24:06        cri

A bisa bayanan da mashirya bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na Beijing na 2019 suka fitar a jiya Litinin, tun bayan da aka bude bikin a ranar 29 ga watan Afrilu an samu masu ziyara sama da miliyan 1.81.

Muhimman wuraren karbar baki hudu na bikin sun karbi bakuncin masu ziyara kusan miliyan 4.48, daga ciki akwai rumfar China Pavilion wacce ta samu masu ziyara kusan 1.36, in ji Ye Dahua, mataimakin daraktan shirya bikin bajekolin.

Ye ya ce, an gudanar da wasu shagulgula kimanin 675 wadanda suka ja hankalin 'yan kallo kimanin 910,000.

Za'a gudanar da ranar China Pavilion a ranar 6 ga watan Yuni, in ji Yu Jianlong, babban kwamishinan China Pavilion. Ana sa ran kimanin mahalarta 950 daga ciki da wajen kasar Sin ne za'a gayyata domin kallon wasannin da za a shirya da kuma halartar bikin nune-nunen furanni a rumfar ta China Pavilion, in ji Yu.

Bikin mai taken "Raya lambuna, Rayuwa mai dadi," bikin baje kolin zai ci gaba da gudana har zuwa ranar 7 ga watan Oktoba kuma a yayin baje kolin nau'ikan furanni masu yawa, da bishiyoyin kayan marmari, da magungunan gargajiya na kasar Sin da fasahar shuka tsirrai, da kuma samar da shawarwari game da raya lambunan shakatawa da dai sauransu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China