Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Guinea-Bissau ya jinjina tsarin hadin gwiwa maras tsoma baki cikin harkokin cikin gida da Sin ta dauka tsakaninta da kasashen Afrika
2019-06-25 13:34:36        cri

An kaddamar da taro tsakanin jami'an hukumomin kudi na kasar Sin da masu tabbatar da sakamakon da aka samu a taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, a jiya Litini a nan birnin Beijing. Shugaban tawagar kasar Guinea-Bissau, kana babban sakataren kula da harkokin waje da hadin gwiwa da kasashen ketare da 'yan kasar mazauna ketare, Mista Dino Seidi, ya halarci taron, inda ya shedawa wakilin CRI cewa, yana jinjinawa tsarin hadin kai maras tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen Afrika da Sin take dauka.

Mista Dino ya kara da cewa, Guinea-Bissau na dora muhimmanci sosai kan bunkasuwar aikin gona, kuma tana matukar bukatar dogaro da kanta wajen biyan bukatun hatsi a gida. Ya ce Sin na da isashen fasahohi da kimiyya a wannan fanni, don haka, a ganinsa, hadin gwiwar bangarorin biyu na da amfani sosai wajen warware matsalar da kasar ke ciki, a sanadin haka, huldar kasashen biyu ta rika samun ci gaba a shekarun baya-baya.

Ban da wannan kuma, Mista Dino ya ce, manyan matakai 8 na hadin gwiwa da Sin ta dauka kan Afrika da shugaba Xi Jinping ya gabatar, sun bayyana kyakkyawan fatan kasar Sin ta fuskar hadin kanta da kasashen Afrika. Ya ce, kasarsa na kokarin tsara manufofi don tabbatar da wadannan manyan matakai 8. Tsarin hadin kai da Sin ke dauka tsakaninta da kasashen Afrika na karfafawa kasar gwiwa kwarai da gaske. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China