Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Beijing za ta kara fadada bude kofar bangarenta na bada hidimomi
2019-08-16 12:20:10        cri
Hukumar kula da harkokin cinikayya ta birnin Beijing, ta ce birnin ya gabatar da wani tsari na shekaru 3, da nufin kara bude kofa da aiwatar da gyare-gyare a bangaren samar da hidimomi.

Tsarin ya kunshi matakai 190 na kara bude kofa a fannonin bada hidima guda 8, da suka hada da kimiyya da fasaha da harkokin intanet da hada-hadar kudi da ilimi da al'adu da yawon bude ido da kiwon lafiya da ayyukan kwararru.

Za a dauki matakan a bangaren bada hidimar kwararru ne domin karfafa hadin gwiwa da hukumomin kwararru na kasa da kasa, kamar ta lauyoyi.

Ta hanyar saukaka matakai masu tsauri da bada damar shiga kasuwa ga masu zuba jari na kasashen waje, birnin Beijing ya samu karin sabbin 'yan kasuwa na ketare, ciki har da hidimomin sayen mota bisa rance na kamfanin Toyota da sabon reshen kamfanin BMW mai bada hidimomin kasuwanci akan intanet. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China