![]() |
|
2019-09-23 20:25:02 cri |
Yau Litinin 23 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin na son yin amfani da damar halartar taron kolin MDD, a fannin ayyukan tinkarar sauyin yanayi, wajen hada kai da sassa daban daban, don kafa kyakkyawar duniya mai tsabta.
A yau ne za a bude taron kolin a birnin New York na kasar Amurka. Kafin hakan, a kwanakin baya, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce jagorancin da kasar Sin take yi wajen tinkarar sauyin yanayi yana da matukar muhimmanci. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China