Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu jarin waje suna kara zuba jari kan hannayen jarin Sin masu daraja na A
2019-09-23 21:08:41        cri

An fara aiwatar da manufar hade alkaluman hannayen jarin Sin masu daraja na A cikin alkaluman S&P Emerging BMI da ake amfani da su a kasuwannin duniya. Ta haka dukkan manyan kamfanonin alkaluman hannayen jari na duniya guda 3, sun hade alkaluman hannayen jarin Sin masu daraja na A cikin alkalumansu da ake amfani da su a kasuwannin duniya, lamarin ya nuna cewa, kasuwannin jarin kasar Sin, da tattalin arzikin kasar suna kara jawo hankalin kasa da kasa.

Kaza lika masu jarin waje suna kara cimma daidaito kan zuba jari a hannayen jarin Sin masu daraja na A. Yayin da ake kara fama da matakn ba da kariya, da nuna bangaranci a duniya, kuma tattalin arzikin duniya na fuskantar barazanar koma-baya, masu jarin waje ba kawai suna sha'awar zuba jari a hannayen jarin Sin masu daraja na A ba, har ma sun nuna karfin zuciya kan tattalin arzikin kasar ta Sin.

A daya bangaren kuma, yadda suke zuba jari a kasar Sin zai yi amfani wajen kara raya kasuwannin jarin kasar Sin. Yadda kasar Sin take jawo jarin waje sosai ya nuna kuzarinta wajen raya tattalin arzikinta, ya kuma ba da tabbaci a kasuwannin jarin duniya da tattalin arzikin duniya. Ana kara cimma daidaito a duniya kan zuba jari a kasar Sin tun da wuri. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China