Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cinikin Wajen Kasar Sin Na Kara Samu Inganci
2019-09-09 20:27:22        cri

 

A cikin watanni takwas na farkon shekarar da muke ciki, jimillar kudin da kasar Sin ta samu a cinikin kayayyakin shigi da fici ta kai RMB triliyan 20.13, karuwar kashi 3.6 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara. Wannan ya nuna cewa, yanayi mai inganci da tattalin arzikin kasar ke ciki bai sauya ba, kana cinikin wajen kasar na kara samun ingancin yadda ya kamata, hakan na nuna cewa, makomar tattalin arziki zai yi kyau a nan gaba.

Manufar kasar Sin ta tsayawa kan kara bude kofa ga kasashen ketare ta ciyar da cinikin waje gaba. A sa'i guda kuma, kamfanonin kasar Sin na kara samun ci gaba, matakan da suka kara azama ga cinikin waje.

 

A yanayin da duniya ke kara fuskantar rashin tabbas, karuwar ingancin cinikin wajen Sin zai amfanawa kamfanoninta wajen gaggauta yin kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasaha, da kuma kara karfin tinkarar hadari. Duk halin da kasashen duniya suka shiga, tattalin arzikin kasar Sin na iya jure jarrabawa da zai fuskanta, zai kuma kara samun ci gaba mai inganci a nan gaba. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China