Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Sin ta sha alwashin kara bude kofa da inganta muhallin zuba jari
2019-08-22 14:54:36        cri

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce za a ci gaba da daukar matakan da suka wajaba, don ganin kasar ta samar da damammaki na zuba jari daga waje, da gina kyakkyawan yanayi, wanda zai ba da damar takara a mataki na kasa da kasa.

Da yake tabbatar da hakan yayin wani taron karawa juna sani da ya gudana, mataimakin minista a ma'aikatar cinikayyar kasar Qian Keming, ya ce Sin za ta ci gaba da samar da damammakin zuba jari ga kamfanoni na kasa da kasa, da zakulo hanyoyin inganta muhallin zuba jari, cikin adalci, kuma a bude, wanda kuma za a iya fahimtar yanayin sa.

Qian ya ce kamfanonin kasa da kasa muhimman abokan hulda ne, dake ganin halin da ake ciki a Sin, suna kuma ba da gudummawa, tare da cin gajiya daga manufofin Sin na gudanar da gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje cikin shekaru 40 da suka gabata.

Wasu alkaluman ma'aikatar cinikayyar Sin sun nuna cewa, kimanin manyan kamfanoni 490, cikin kamfanoni mafiya girma 500 dake sassan duniya ne suka zuba jari a kasar Sin. Burin kasar Sin na jawo hankulan masu zuba jari na kasa da kasa, na da nasaba da kudurin kasar na dunkulewa da sauran manyan kamfanonin kasa da kasa, da samar da alfanu gare su, domin kara inganta ayyukan bude kofa, da fadada cudanya a bangarorin zuba jari da hada-hadar cinikayya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China