Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An harbe shugabannin kungiyar Boko Haram 7 har lahira
2019-09-21 16:37:22        cri
Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa, sojojin kasar da sojojin kawance na kasa da kasa sun kai harin hadin gwiwa kan sansanin kungiyar Boko Haram dake yankin tabkin Chadi a kwanakin baya, wanda ya kai ga harbe shugabanni 7 na kungiyar har lahira.

A cikin sanarwar da ta fitar a jiya, rundunar ta ce, sojojinta da sojojin hadin gwiwa na kasashen Nijeriya, da Kamaru, da Nijer, da Chadi da sauransu sun kai harin igogi da luguden wuta ta sama kan sansanin kungiyar Boko Haram. Bisa labarin da kungiyar Boko Haram ta bayar, shugabanni 7 na kungiyar sun mutu a sakamakon harin.

Sanarwar ta kara da cewa, sojojin za su ci gaba da kai hari kan kungiyar a wannan yanki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China