Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FRSC ta fara wani shirin sintiri na musamman don rage aukuwar hadurra a hanyoyin Najeriya
2019-09-19 09:49:46        cri
Jami'an hukumar kiyaye hadurra a kan tituna dake Najeriya (FRSC) sun fara wani sintiri na musamman da ya kunshi ilimantar da direbobi, a wani mataki na rage aukuwar hadurran a kan titunan kasar.

Mai magana da yawun hukumar Bisi Kazeem shi ne ya sanar da hakan, yana mai cewa, shirin na daga cikin matakan da hukumar ta dauka, don rage yawan hadurran dake faruwa, galibin sakamakon tukin ganganci.

Ya ce, bayan fara shirin sintirin na musamman, babban jami'in hukumar ya umarci jami'an hukumar dake shiyyoyin kasar, da su sanya ido kan manyan titunan kasar, ta hanyar gudanar da sintiri yadda ya kamata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China