Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jumia yana kokarin bunkasa yawon bude ido a Najeriya
2019-09-19 10:47:45        cri
Kamfanin hada-hadar cinikayya ta intanet mafi girma a Afirka wato Jumia, ya bayyana cewa, yana nan yana shiryen-shiryen kaddamar da bikin ranar yawon bude ido ta duniya na farko, domin wayar da kan jama'a game da muhimmancin yawon bude ido a Najeriya.

Shugaban tafiye-tafiye na kamfanin Jumia, Omolara Adagunodo shi ne ya sanar da hakan, cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, yana mai cewa, an shirya gudanar da bikin ne a birnin Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya.

MDD dai ta kebe ranar 27 ga watan Satumban kowace shekara, a matsayin ranar yawan bude ido ta duniya, don kara ilimantar da al'ummar duniya game da muhimmancin yawon bude ido.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China