Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu rahoton bullar cutar shawara a jihar Gomben Najeriya
2019-09-20 09:37:37        cri

Rahotanni daga tarayyar Najeriya sun tabbatar da cewa, mutane 6 sun kamu da cutar shawara a jihar Gombe dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Jami'i a hukumar lafiya ta jihar Nuhu Vile, ya shaidawa manema labaru cewa, yanzu haka an baiwa mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar magana har ma an sallame su daga asibiti.

Tun a ranar 29 ga watan Agustan wannan shekara ce dai, aka ba da rahoton bullar cutar a yankin arewa maso gabashin kasar, ciki har da jihohin Bauchi da Borno. Sai dai babu wanda ya mutu a jihar sanadiyar cutar. Yana mai cewa, binciken da masana suka gudanar ya nuna cewa, cutar ta samo asali ne daga Yankari, dake makwabtaka da jihar Bauchi.

Yanzu haka, gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti, don magance wannan matsala, don haka, ya yi kira ga jama'a, da a kullum su rika hanzarta sanar da cibiyoyin lafiya rahoton bullar cutar, don a duba lafiyarsu a kuma ba su maganin da ya dace.

A cewarsa, sauro ne yake haddasa cutar ta shawara, don haka, ya bukaci jama'a da su rika tsaftace muhallinsu.

Ya ce, da zarar an yi wa jariri ko jaririya rigakafi kafin su kai watanni 9, akwai yiwuwar samun kariya daga kamuwa da cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China