Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 8 sun jikkata yayin da zanga zanga ta kara Kamari a HK
2019-09-16 10:15:38        cri
Mutane a kalla 8 ne suka raunana a jiya Lahadi, yayin da masu zanga-zanga suka kara kaimi ta hanyar kunna wuta da jifa da bam na fetur da dukan mazaunan da ba su ji ba, ba su gani ba da toshe tituna a tsibirin HK.

Zanga-zanga a tsibirin HK ya sake rikidewa zuwa rikici a jiya, inda masu zanga zangar suka fara jifa da bam na fetur a yankunan dake kewaye da ofisoshin gwamnatin musamman na yankin da majalisar dokoki da misalin karfe 4:30 na yamma, tare da lalata tasoshin jirgin kasa.

Gargadin da aka yi ta yi ga masu zanga zanga dake zaman barazana ga 'yan sanda da al'umma ya ci tura, domin sai da 'yan sandan suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da motocin hana barkewar rikici a taron jama'a, a yankin tsakiya da na hada-hadar kasuwanci na tsibirin HK.

Daga nan ne kuma masu zanga-zangar suka koma yankin gabas, inda suka taru a wuraren da suka hada da Wan Chai da Causeway Bay da North Point, tare da ta da rikici.

'Yan sanda sun ce ayyuka masu zanga-zangar sun saba doka, kuma suna barazana mai tsanani ga tsaron al'ummar dake wuraren, inda suka gargade su da su dakatar da ayyukan nasu nan take. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China