Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu tsiraru masu zanga zanga na fatan gurgunta "tsarin kasa daya salon gudanarwa 2" na Hong Kong, in ji Yang Guang
2019-09-03 19:16:24        cri
Kakakin ofishin majalissar gudanawar kasar Sin mai lura da al'amuran Hong Kong da Macao Mr. Yang Guang, ya ce burin wasu tsirarun masu zanga zanga a Hong Kong shi ne yin fito na fito da gwamnatin tsakiyar Sin, da kuma samun ikon cin gashin kai, tare da gurgunta "tsarin kasa daya salon gudanarwa 2" da yankin Hong Kong ke aiwatarwa.

Mr. Yang Guang wanda ya yi wannan tsokaci a Talatar nan yayin wani taron manema labarai, ya ce wadannan tsageru na son jefa yankin Hong Kong cikin hargitsi, da dakile harkokin gudanarwar yankin, da kwace ikon mulkinsa, matakin da a burinsu zai kai ga baiwa Hong Kong din wata dama ta cin gashin kai, ko matsayi na sarrafa harkokinsa da kansa a fannin siyasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China