Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Hongkong ta yi tir da matakin karya doka da wasu masu zanga-zanga suka dauka
2019-07-29 10:31:27        cri

A jiya Lahadi, wasu mutane sun yi zanga-zanga a wasu sassa na tsibirin Hongkong ba tare da samun izini ba, inda suka yi watsi da doka, suka dauki matakin nuna karfin tuwo tare da kowa illa ga yanayin zaman lafiya da ake ciki a yankin. Sakamakon haka, a sanyin safiyar yau, kakakin gwamnatin yankin Hongkong ya yi tir da laifuffukan da suka aikata.

Kakakin ya ce, a jiya, wasu masu zanga-zanga sun dauki matakan nuna karfin tuwo a yankunan dake Sheung Wan da gundumar yammacin yankin, inda suka rika jifan 'yan sanda da tubala, da kona abubuwa, da yiwa 'yan sanda da sauran mazauna yankin Hongkon barazana. Sabo da haka, gwamnatin yankin musamman ta Hongkong ta yi tir da irin wadannan matakan haddasa tashin hankali a cikin al'umma da aka dauka ba tare da yin la'akari da doka ba. Kakakin ya kara da cewa, gwamnatin yankin musamman ta Hongkong, za ta ci gaba da nuna goyon baya ga 'yan sanda da su sauke nauyin dake bisa wuyansu bisa doka, ta yadda za a hana sake faruwar matakan nuna karfin tuwo domin hanzarta dawo da oda a cikin al'umma kamar yadda ya kamata.

Bangaren 'yan sandan yankin Hongkong ya bayyana cewa, a yayin al'amarin da ya auku a ran 28 ga watan, hukumar 'yan sanda ta tsare mutane a kalla 49 wadanda suka aikata laifuffukan shirya zanga-zanga ba tare da samun izini ba, da boye makaman da za a iya yin amfani da su wajen kai farmaki. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China