Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe na shirin kwashe jama'arta daga Afrika ta kudu
2019-09-12 10:30:24        cri

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanar a jiya Laraba cewa, tana shirin kwashe jama'arta dake Afrika ta kudu, sakamakon yadda 'yan kasashen biyu suka rasa rayukansu, a wata tarzomar nuna kyamar baki da ta barke a Afrika ta kudu.

Hakan dai ya sanya Zimbabwe zama kasa ta biyu bayan Nijeriya, da ta sanar da janye jama'arta daga Afrika ta kudu. Amma har ila yau, ofishin jakadancin Zimbabwe dake Afrika ta kudu bai mayar da martani ga lamarin ba, kuma bai fitar da ajandar janye jama'ar kasar sa ba tukuna. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China